N’KONNI, NIGER - Yanzu haka dai, ‘yan Nijar da dama ne suka soma kokawa game da dimbin matsalolin rayuwa da suka dabaibaye al'amuran su na yau da kulum, tun bayan matsalar harbawar kudin biredi a makon jiya, matsalar iskar gas da jama'ar kasar ke anfani da shi wajen yin girki, ko aikin daji ko a wuraren sana'o'in su, yayi ko sama ko kasa a wadansu yankunan kasar, yayin da farashinsa ya kai koluluwa, kuma ya fi karfin talaka a wadansu yankuna na Nijar.
Yanzu haka kilo shida da ya kamata a ce an sayar a dokance, sefa jaka daya ba dala 40, ya kai jaka shida a manyan garuruwa kamar Birni N'Konni.
Muyar Amurka ba ta iya tantance masababin tashin farashin gas din ba, kasancewa 'yan kasuwa da masu amfani da shi basu da wani kwakkwaran bayani.
Ana cikin hakan ne, sai ga farashin man Diezel ya haura, ko a wuraren da hukumomin kasar suka baiwa izinin sayar da shi, kamar yanda wakilin Sashen Hausa ya iske wadansu masu manyan motoci na dakon kaya da na daukar kasa, sun yi fuskar shanu don rashin samun man na Diezel a wannan ranar.
Masu tankar mai, sun ce su dakon kaya ne suke yi, amma mu tambayi masu gidajen su ko ma'aikatar rumbun ajiyar mai na sayar da shi ta kasa.
Wannan lamarin inji wani ‘dan fafutukar farar hulla mai kula da yakin kwato hakkokin dan Adam, yayi muni.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5