Kamfanin dillancin labarai na AFP ne ya ruwaito hakan daga ofishinsa na birnin Paris da ke Faransa.
Harin dai ya rutsa har da wasu ‘yan kasar Nijar biyu da ke yin rakiya ga Faransawan.
Ya kuma auku ne a kauyen Koure da ke a da tazarar kilomita 60 da birnin Yamai fadar gwamnatin Jmhuriyar Nijar abin da masu fashin baki akan sha’anin tsaro ke cewa bai zo da mamaki ba.
Gidan talbajin din France 24 mallakar gwamnatin Faransa, ya ruwaito a ranar Juma’a cewa kungiyar ta IS ta ce reshenta na Yammacin Afirka ne ya kai harin akan ma’aikatan agajin kamar yadda wata sanarwa da kamfanin nan mai bin diddigin ala’muran masu tsattsauran ra’ayi na SITE Intelligence Group ya wallafa a ranar Alhamis.
Kokarin jin ta bakin Ministan Tsaron kasar Nijar Farfesa Isuhu Katambe da kakakin gwamnati Zakariyya Abdurrahman dangane da wannan lamari ya cutura, domin ba su amsa wayarsu ba kuma ba su ba da amsar sakonnin waya da aka aika masu ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Wannan dai ba shi ne karon farko da kungiyar ta IS ke daukan alhakin muggan hare-hare da ake kai wa a yankin Sahel ba lamarin da ya sa jama’a ke kara kira ga hukumomi da suka kara daukan tsaurara matakan tsaro a tsakanin kasashen yankin.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5