A daya bangaren kuma, shugaban rundunar sojin kasar Iran, ya yi watsi da tayin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi, na tattaunawa kai-tsaye da shugabannin Iran, yana mai cewa Tehran ba za ta taba amincewa ta gana da abin ya kira “Babban Shaidani ba”
Babban kwamandan rundunar tsaro da ake kira Islamic Revolutionary Guards a turance, ko kuma IRGC a takaice, Mohammad Ali Jafari, ya bayyana hakan a wata budaddiyar wasika da aka wallafa shafin kamfanin dillancin labaran Fars News Agency na gwamnatin Iran.
A cikin wasikar, Jafari, ya kara jaddada cewa Iran ba za ta taba tattaunawa da Amurkan ba, wacce ya wa lakabi da babbar shaidaniya, domin dogaro da addinin Islama da kasar ta Iran ta yi, ya sa “ta sha banban da sauran kasashe masu mika wuya ga Amurka” kamar yadda ya rubuta.
Kwamandan rundunar sojin ta Iran ya kuma kwatanta shugaba Trump a matsayin “dan koyon shugaba” wanda burinsa na ganin jami’an Iran sun nemi a tattauna da su, zai bi shi “har kabari.”
Jafari, shi ne babban jami’i a kasar ta Iran da ya mayar da martani kai-tsaye ga tayin da shugaba Trump ya yi a ranar Litinin, a wani taron manema labarai a Fadar White House, inda ya ce zai tattauna da shugabannin Iran kan shirin nukiliyanta, ba tare da gindaya wasu sharudda ba.