Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tace a Shirye Take ta Gana da Iran


Jiya litinin Shugaban Amurka Donald Trump yayi wani cikakken bayani da bai taba yi ba a baya cewa, a shirye yake yayi ganawar kai-tsaye da Iran.

A lokacin wani taron manema labarai na hadin guywa da firayin ministan kasar Italiya, Giuseppe Conte, wani dan jarida ya tambayi Trump ko zai iya ganawa da shugaban Iran Hassan Rouhani?

“Na yarda da zaman tattaunawa,” amsar da Trump ya maida kenan. Ya cigaba da cewa, “yin magana da mutane, musamman idan akan batutuwan da za iya kawar da yaki, mace-mace, yunwa da kuma sauran wasu abubuwa ne, ai sai a gana. Babu wani aibi a zaman tattaunawa.

Trump ya ambaci tattaunawar ido-da-ido da yayi kwanan nan da shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un da na Rasha Vladimir Putin a matsayin misalin matakin diplomasiyyar kai tsaye da ya dauka akan shugabannin da aka dauka a matsayin masu adawa da muradan Amurka.

Da aka tambaye shi ko yana da wasu bukatu da zai nema daga Iran kafin tattaunawar, sai ya ce babu wasu ka’idoddi Idan Iran tana so a tattauna, zan tattauna.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG