Dubban masu goyon bayan gwamnatin Iran ne suka gudanar da gangamin kwanaki uku a jere a wurare da dama a cikin Tehran da sauran Birane bayan babban jagoran kasar Ali Khamenei ya bukaci hukumomin kasar da su dauki mataki kwakwkwara akan wadanda suke da hannu wajen tada zaune tsaye da aka kwashe mako ana gudanar da gangamin kin jinin gwamnati.
Wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 22 da kuma kame dubbai a sauran wurare. Jami’an Iran sun ce wannan shirin hukumar leken asirin Amurka ta CIA ne, tare da Isra’ila da ma Saudi Arabiya, wadanda sune suke da alhakin barkewar tashe-tashen hankula kan makwabtan kasar Iran tun daga nasarar da Donald Trump yayi ta zabe.
Babban Malami Ahmad Khatami ya fadawa masu ibada a Jami’ar Tehran cewa, “Ya kamata a dauki kwakwkwaran mataki akan wadannan Iraniyawa wadanda masu goyon bayan Amurka suka yaudara, sannan hukunci kamar yadda addinin Islama ya tanada.”