Iran zata bayyana ci gaban ayyukan nukiliya da ta samu

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad yace kasar tana dab da sanar da ci gaban da ta samu a ayyukan nukiliya

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad ya sanar yau asabar cewa, Iran zata gabatar da wadansu muhimman ayyukan nukiliya cikin ‘yan kwanaki kalilan masu zuwa.

Mr. Ahmadinejad ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a fitaccen dandalin nan Azadi yayin gangamin cika shekaru 33 da juyin juya halin Islama da aka yi a kasar.

"Insha Allah, a cikin kwanaki masu zuwa, duniya zata ga Iran tana nuna ci gaban da ta samu a fannin ayyukan nukiliya"

Shugaban kasar Iran din dai bai yi karin haske dangane da ayyukan nukiliyan da ya ambata ba.

Kasashen yammaci sun hakikanta cewa, Iran tana gudanar da ayyukan nukiliyan ne da nufin kera makaman nukiliya, zargin da Iran ta musanta da cewa aikin nukiliyanta na zaman lafiya ne.

Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai sun tsawata takunkumin tattalin arziki kan Iran a yunkurin ganin kasar ta koma teburin tattaunawa da nufin kawo karshen ayyukanta na nukiliya.