SHI’A: Iran tana iya neman bayani daga Najeriya
Wani lauya mai zaman kansa a Najeriya, Aliyu Abdullahi yace dokar kasa da kasa ta hana kasashe yiwa kasa mai diyauci katsalandan.
Da yake tsokaci dangane da bayanan dake nuni da cewa, Iran ta gayyaci jakaden Najeriya ya yi mata bayani kan hatsaniyar da ta auku tsakanin ‘yan Shi’a da sojojin Najeriya, tare kuma da gindayawa Najeriya sharuda, Barrista Abdullahi yace wannan doka ta haramtawa kasasahe katsalandan a harkokin da basu shafe su ba.
Sai dai yace dangantaka dake tsakanin Najeriya da Iran na iya bata damar ta nemi bayanai daga kasar dake abota da ita da nufin kara fahimtar juna da kuma tafiya tare.
A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Aliyu Abdullahi ya bayyana takaicin arangamar da yace ana bukatar taka tsantsan da kuma daukar matakan ganin lamarin bai sake aukuwa ba.
Ga bayanin Aliyu Abdullahi.
Your browser doesn’t support HTML5