Trump ya ce “ba a sami asarar rayukan amurkawa ko ‘yan Iraki ba, saboda matakin da aka dauka, na kare sojojin da kuma tsarin gargadin gaggawa da ke aiki sosai,” ya kara da cewa barnar da aka samu ba wata mai yawa bace sosai.
A jawabin na Trump, ya nuna alamun Amurka ba zata ta dauki matakin soji domin mayar da martani kan hare-haren ba, amma maimakon haka, Amurka za ta ‘kara kakabawa Iran takunkuman tattalin arziki masu tsauri, domin ci gaba da ruguza tattalin arzikinta.
Biyo bayan hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kaiwa sojojin Amurka a Iraki da jawabin shugaban Amurka Donald Trump na jiya Laraba, masana sunce sun yi imanin kasashen biyu ba zasu tsananta lamarin ba, bayan mutuwar babban kwamandan Iran Qassem Soleimani sanadiyar harin da Amurka ta kai ta sama makon da ya gabata.
A martanin kashe Soleimani da aka yi, rundunar dakarun juyin-juya halin Iran ta dauki alhakin kai hare-haren makamai masu linzamin sama da dozin guda da suka auna sansanonin biyu a Iraki da sojojin Amurka ke zaune.
Ana daukar Soleimani a matsayin babban mai fada aji bayan shugaban addini Ayotallah Ali Khamenei a Iran.