Iran Ta Musanta Harbo Jirginta Mara Matuki Da Amurka Ta Yi

A yau Jumma’a Iran ta fada cewa bata rasa ko daya daga cikin jiragenta marasa matuka ba, ta na mai musanta wasu rahotanni daga Amurka da ke cewa, wani jirgin ruwan yakin Amurka ya harbo wani jirgin Iran mara matuki a Mashigin Homuz.

Mataimakin ministan harkokin ajen kasar Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da haka a lokacin da ya rubuta a shafin sa na Twitter cewa, “bamu rasa ko daya daga cikin jiragenmu marasa matuka a Mashigin Homuz ba, ko wani wuri daban.

Ya kara da cewa “yana nuna damuwa, mai yiwuwa jirgin yakin ruwan Amurka ne ya harbor wani jirgin Amurkar mara matuki bisa kuskure.”

Shugaba Donald Trump, ya fada a jiya Alhamis cewa jirgin yakin ruwan Amurka ya harbo wani jirgin Iran mara matuki da yayi wa ma’aikatan jirgin ruwansu barazana a mashigin Homuz.