A yau Talata Iran ta harba makami mai linzami kan Isra’ila, abinda ya sabbaba tashin jiniyar ankarar da kawo hari a birnin Tel Aviv da fadin Isra’ila a cewar ma’aikatar tsaron Isra’ila.
Hakan na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan Israi’la ta kashe shugaban kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah, da kwamandojinsa.
Hezbollh tace ta harba makamin rokar ne tana harin shelkwatar hukumar leken asirin Isra’ila, MOSSAD, wacce take zargi ta kitsa jeren kashe-kashen a kan manyan kwamandojinta a baya-bayan nan da kuma harin fashewar na’urorin sadarwa na makon daya gabata wanda ya hallaka gommai tare da jikkata dubban mutane, ciki harda mambobin kungiyar da dama.
Your browser doesn’t support HTML5
Wuta ta haskaka sararin samaniyar Isra'ila kamar yadda ma'aikatan kafar yada labarai ta NBC dake birnin tel aviv da yankin kan iyakar Lebanon na Tyre suka shaida sanda aka harba makami mai linzamin. An kuma hangi kananan tartsatsin wuta, wanda ake zaton sun taso ne daga kariyar kare makamai ta Isra'ila a yayin da kasar ke kokarin kare kanta daga harin.
An kuma jiyo karar wata fashewa a bidiyon da kafar yada labaran ta NBC ta nada, sai dai ba'a tantance ko karar ta haduwar makamai masu linzami a sararin samaniya ce ko kuma ta saukar makaman ce a cikin isra'ila.
Tunda fari jami'an Amurka sun yi gargadin cewar Iran na shirin harin Isra'ila da makami mai linzami, kamar yadda wani babban jami'in fadar White House dana ma'aikatar tsaron Amurka suka shaidawa kafar yada labaran ta NBC a yau Talata.
Da safiyar yau ne rundunar sojin Isra'ila ta gargadi al'ummomin dake zaune a yankunan kan iyakar Lebanon dasu kaurace daga kusan garuruwa 24 bayan da ta kaddamar da samamen da ta kira da kwarya-kwaryan kutse ta kasa akan mayakan kungiyar Hezbollah