Kasar Iran ta harba makamai masu linzami fiye da goma da safiyar yau Laraba, akan wasu cibiyoyin sojin saman Iraki guda biyu da sojojin Amurka ke amfani da su, wannan wani mataki ne da ya biyo bayan barazanar da shugabannin Iran suka yi na maida martani kan Amurka, saboda hari ta sama da Amurka ta kai, wanda yayi sanadiyyar kisan wani babban kwamandan sojin Iran.
Shugaban Addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya kira matakin kai harin da Iran ta yi a matsayin wani “babban bugu” ga Amurka, kuma ya ce ya kamata a kawo karshen "kasancewar Amurka ta rashin dacewa" a yankin.
Daga baya Shugaban Iran, Hassan Rouhani a shafin sa na twitter ya kara da cewa "matakin karshe da Iran zata dauka" kan kisan kwamandan dakarun juyin juya halin Iran Kassem Soleimani" shine su kori dukkan sojojin Amurka daga yankin."
Ana sa ran Shugaban Amurka Donald Trump zai maida martani akan harin makaman masu linzami da Iran ta kai a cikin wata sanarwa yau Laraba.
A halin da ake ciki kuma, Gwamnatocin kasashen duniya sun yi kira ga Amurka da Iran akan su sassauta zaman fargaban dake faruwa tsakaninsu, biyo bayan wasu jerin hare-hare kan junansu a Iraki.
Shugabar tarayyar Turai ta EU Ursula von der Leyen ta ce "Rikicin na yanzu ba yankin kawai ya shafa ba, har ma da sauran kasashe, kuma dole ne a kawo karshen amfani da makamai ko karfin soja don samar da damar hawa teburin sulhu." Ta kuma ce "ana bukatar mu yi duk abinda ya dace don sake maido da tattaunawa tsakanin kasashen, kuma wannan kiran ba zai taba yin yawa ba."
A yau Laraba Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya Dominic Raab ya yi Allah wadai da harin makamai masu linzami da Iran ta kai kan cibiyoyin jiragen saman na Iraki guda biyu da sojojin Amurka da kuma dakarun hadin gwiwa ke amfani da su, ciki har da sojojin Birtaniyya.