Iran Ta Ce Akwai Yiwuwar Ta Tattauna Da Amurka

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Abbas Mousavi

Mousavi ya fadawa taron manema labarai da aka yada shi kai-tsaye a gidan talabijin na Press TV cewa, tattaunawar da kuma zaman sulhun zai yi wu ne idan aka tsara batutuwan da za a tattauna akai a kuma samu sakamakon mai kyau.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Abbas Mousavi, ya fada yau Litinin cewa, akwai yiwuwar a tattauna tsakanin Iran da Amurka idan har za a mayar da hankali kan ajandar da za ta kai ga samar da sakamako mai kyau, amma a cewar Mousavi, Washington ba ta neman a tattauna.

A baya, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce a shirye yake ya tattauna tare da Jamhuriyar kasar Musulincin ta Iran.

Mousavi ya fadawa taron manema labarai da aka yada shi kai-tsaye a gidan talabijin na Press TV cewa, tattaunawar da kuma zaman sulhun zai yi wu ne idan aka tsara batutuwan da za a tattauna akai a kuma samu sakamakon mai kyau.

Amma a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, “ba a shirye suke a tattauna ba, kuma ba sa neman a yi hakan.”