Manyan jami’an gwamnatin shugaba Barack Obama na fuskantar tambayoyi a gaban ‘yan majalisar dattawan kasar kan yarejejeniyar nukiliyar Iran da aka kulla a farkon watannan a Vienna.
WASHINGTON D.C. —
Wannan shi ne karo na farko da aka gabatar da wannan batu a baina jama’a wanda ‘yan majalisar ke da damar su amince da ita ko kuma akasin haka nan da watan Satumba.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ne ya fara bayyana a gaban kwamitin ‘yan majalisar inda suka zargi shi da cewa sun bari Iran Iran ta yi musu rufa ido.
Amma Kerry duk da cewa Iraniyawa sun sami abinda suke bukata, amma kuma an dakile shirinsu na mallakar nukiliya.
Gabanin halartar wannan taron, Kerry ya bayyana cewa kulla wannan yarjejeniya zai samar da zaman lafiya mai dorewa a duniya.
Yarjejeniyar dai za ta ba da damar a dagewa Iran takunkumin da aka kakaba mata bisa dalilan takaita shirin nukiliyar nata.