Inter Milan Ta Lashe Kofin Serie A, Ajax Ta Lashe Na Dutch League

Dan wasan Inter Milan Lukaku da kocinsa Conte Suna murna

Galabar da Atalanta ta samu, ita ta tabbatarwa da Inter nasararta, abin da ya kawo karshen mallake kofin gasar da Juventus ta yi na wani tsawon lokaci tana lashe kofin.

Bayan shekara 11 da ta kwashe tana farin lashe kofin gasar Serie A ta Italiya, Inter Milan ta cinye kofin a wannan karon.

Ta samu nasarar ce bayan da Atalanta ta gaza lashe wasanta da Sassuolo.

A ranar Asabar kwallayen da Christian Eriksen da Achraf Hakimi suka ci a karawarsu da Crotone ta kara kusantar da ‘yan wasan na Antonio Conte ga lashe kofin inda suka bada tazarar maki 14 tsakaninta da Atalanta,

An tashi da ci 2-0 ne a wasan.

Ita dai Atalanta ta tashi kunnen doki da ci 1-1 tsakaninta da Sassuolo yayin da har yanzu ya ragewa Inter wasa hudu ta kammala a wannan kaka.

Nasarar da Atalanta ta samu, ita ta tabbatarwa da Inter nasararta, abin da ya kawo karshen mallake kofin gasar da Juventus ta yi na wani tsawon lokaci tana lashe kofin.

A can gasar Dutch League na kasar Holland, Ajax ta lashe kofin gasar a karo na 35 a ranar Lahadi, bayan da ta samu nasara akan Emmen da ci 4-0.

‘Yan wasanta Jurrien Timber, Sebastian Haller, Davy Klaassen da Devyne Rensch ne suka zura mata kwallaye a wasan, wanda aka buga shi ba tare da ‘yan kallo a filin wasa ba.

A kakar wasa ta bara, babu kungiyar da ta lashe kofin gasar, saboda dakatar da ita da aka yi sandaiyyar barkewar cutar coronavirus.

A barar, Ajax ce ke gaba a saman teburin gasar ta Dutch.