Mai kamfanin manhajar Instagram Kevin Systrom ya ce muhimmin abu ne a garesu su ga cewa manhajar ta taimakawa lafiyar kwakwlwar masu amfani da ita.
A wata hira ta musamman da shirin Newsbeat na BBC don tallata sabon salon IGTV Da ya fito da shi, ya ce: “za mu tabbatar da cewa muna taka muhimmiyar rawa a duniya." An sha nuna cewa Instagram shine shafin sada zumunci mafi muni a bangaren lafiyar kwakwalwar matasa.
Kamfanin ya sanarda fito da wata sabuwar dabara da za ta sa masu amfan ida shafin su dade akansa.
Dabarar IGTV na ba masu amfani da shafin damar sanya abubuwa da za su kai tsawon awa daya.
"Bayanai sun nuna cewa mutane na jin dadin amfani da Instagram sosai musamman idan abubuwan da abokansu suka sanya ba su bace masu ba," a cewar Kevin.
Ya kuma ce, dalilin da ya sa muka koma amfani da sabuwar dabarar shine don mun gano cewa abubuwa dayawa na bacewa mutane daga abokanan su, don haka mu ka sa dabarar da zata a iya ganin abubuwanda aka sanya a baya.
Kevin ya kuma yarda da sukar da ake yiwa kamfanin amma ya ce ba za a iya ganin canji ba nan take, ma'ana sai nan gaba.