Euro 2024: Ingila Za Ta Kara Da Sifaniya A Wasan Karshe Bayan Ta Doke Netherlands

Tawagar kwallon kafar Ingila ta kai wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai bayan ta yi waje da takwararta na Netherlands.

Wasan da ya wakana a filin wasan Westfalenstadion na birnin Dortmund ya tashi ci 2-1 inda Xavi Simons ya farke wa Netherlands minti 7 da fara wasa.

Kyaftin din Ingila, Harry Kane, ta bugun da ga kai sai mai tsaron raga, ya zura wa Ingila a dai dai minti 18.

Bayan hutun rabin lokaci Ollie Watkins, wanda ya shigo wasan a minti 81, ya farke wa Ingila a minti na 90.

A jiya Talata, Tawagar kwallon kafar Sifaniya ta kai wasan karshe a gasar bayan ta ci Faransa 2-1 a filin wasa na Allianza Arena a birnin Munich na Kasar Jamus.

Sakamakon wasannin, Sifaniya da Ingila za su fafata ranar Lahadi 14 ga watan Yuli a wasan karshe wanda za a buga karfe 8 na dare agogon Najeriya da Nijar a filin wasa na Olympiastadion da ke birnin Berlin.