Mutane dayawa na ganin daukar nauyin daliban Najeriya zuwa kasashen waje karatu ci gaba ne ta fuskar bunkasa ilimi, amma masana ilimi sunce mayar da hankali wajen inganta jami’o’in cikin gida Najeriya shine yafi muhimmanci.
A karshen makon da ya gabata ne ‘dan Majalisar Wakilan Najeriya, Abubakar Ladan Sule Ja, ya dauki nauyin tura wasu ‘daliban yankinsa su 18 zuwa Jami’ar Al-Azhar dake kasar Masar. Yace dalilin da yasa shine kasancewar yadda ilimi a Najeriya ya zama abin wahala hakan yasa suka aika yaran domin samo ilimiin da zai taimakawa kasa da al’umma baki daya.
To sai dai kuma malami a sashen ilimin manya a jami’ar Usman Dan Fodiyo dake Sokoto, Abdullahi Umar Alhassan, yace mayar da hankali wajen inganta jami’o’in dake cikin gida Najeriya shine yafi muhimmanci, haka kuwa zai hada da samar da kayan aiki da isassun malamai da horar da su, ta yadda jami’o’in Najeriya zasuyi gogayya da sauran jami’o’in duniya.
Daliban da suka sami wannan tallafin dan Majalisa Abubakar Ladan, sun baiyana farin cikin su kasancewar sun dade suna neman wannan dama. Inganta ilimi ta kowacce fuska nada muhimmanci kamar yadda masu iya magana ke cewa “Ilimi gishirin zaman duniya”.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5