Alkaluman kungiyar yaki da cutar sukari sun bayyana cewa mutane kimanin Miliyan 382 ne suka kamu da cutar Diabetes a duniya cikin shekarar 2013, kuma idan ba dauki mataki ba yawan masu fama da cutar zai haura zuwa Miliyan 592 a shekarar 2035. Sakamakon lura da yadda cutar ke boye kanta ba tare da wanda ke dauke da ita ba ya gano hakan ba har sai tayi nisa.
Hakan yasa gwamnatin Nijar da hadin gwiwar wasu kungiyoyi suka bullo da wani shirin gwajin jini da bayar da magunguna kyauta a fadin kasar.
Daya daga cikin masu jan akalar shirin kuma kwararren likita mai kula da masu cutar sukari a babban Asibitin Yamai, Dakta Mohammad Sani Mohamman Aminu, yace a nahiyar Afirka mutane Casa’in cikin Dari basu san suna dauke da cutar sukari ba, hakan yasa suke kira ga kowa da kowa ya fito domin ayi masa gwaji.
Hukumomin kiwon lafiya sun dauki alkawarin bayar da kulawar da ta dace ga wadanda ayyukan gwajin suka tabbatar suna da wannan cuta ta sukari, kasancewar an samu wasu mutane masu yawa dauke da ita, yanzu haka an basu shawarar irin abincin da ya kamata su fara amfani da shi.
A jawabin da yayi albarkacin wannan rana Ministan kiwon lafiya na Nijar Dakta Iliyasu Idi Mai Nasara, ya gargadi jama’a suyi gwajin jini domin tantance halin da ake ciki domin tantance halin da suke ciki game da wannan cuta, wacce aka gano tana hallaka mutum daya a duniya a kowanne dakikoki Shida, kuma akan haifi yara kanana da wannan cuta.
Domin karin bayani.