Yanzu haka Jam'iyar MRDD ta garzaya babban kotun jihar Adamawa, inda ta nemi da a dakatar da zaben jihar da za’a gudanar na ranar 23 ga wata Maris bisa zargin ba a saka alamar jam'iyyar ba a zaben gwamna da aka yi tun farko.
Kotu ta umarci hukumar zabe ta INEC da ta dakatar da zaben har sai an yanke hukunci.
Sai dai kuma a taron manema labarai da hukumar ta kira, kwamishinan hukumar zaben jihar, Barrista Kassim Gana Gaidam, ya ce yanzu haka sun sami wannan umarnin kuma hukumar ita ma ta shirya tsaf domin kalubalantar umarnin a gaban kotu.
A yau Alhamis ake shirin fara sauraren karar.
Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyar PDP, Ahmad Umaru Fintiri, shi ne ya ke kan gaba a zaben da aka yi, inda ya yiwa gwamnan jihar na jam'iyar APC fintinkau da kusan kuri'u dubu talatin da doriya.
Sakataran Tsare-Tsare na jam’iyyar APC a jihar Adamawa, Hon. Ahmad Lawal, ya ce sun shirya shiga wannan zabe muddin kotu ta ce a gudanar da shi, kuma a shirye su ke domin su ga sun lashe zaben gwamnan da za a kammala.
Yanzu haka dai jam'iyar PDP ta samu yawan kujeru 11 cikin 25 na kujerun majalisar dokokin jihar, inda itama jam'iyar APC da ada kujerunta ne baki daya itama ta sami kujeru 11.
Yayin da sabuwar jam'iyar ADC ta samu kujera daya, sannan kuma za'a kammala na saura kujeru biyu a wannan asabar.
Saurari cikakken rahotn Ibrahim Abdulazizdaga Yola:
Your browser doesn’t support HTML5