Kamar yadda Alhaji Hassan Ahmad Mahuta, kwamishinan hukumar zabe a Jihar Kaduna ya shaidawa Muryar Amurka.
“Katuttuka da muka samu gaba da shine miliyan uku da dubu dari uku da sittin da daya, adadin katuttukan da aka kawo Kaduna kennan a rabawa masu jefa kuri’a”, a cewar Mr. Mahuta.
Alhaji Mahuta ya kara da cewa “to daga cikin wadannan, mun rabar da miliyan uku da dubu dari da ashirin da shida, da dari bakwai da tara, wanda yayi dai-dai da kashi 93 cikin dari na katuttukan da aka kawo. Saura kashi 7 ne ya rage ba’a raba ba, kuma ana nan ana jiran masu su suzo su karba a kowace mazaba”.
Game da batun sayar da kati, kwamishina Mahuta yace “idan wani yazo da katin wani a ranar zabe, ba zai iya amfani da shi ba, saboda muna da wata na’ura wadda zata gwada abubuwa guda uku. Na daya dai, zata tantance wannan katin da ka kawo, lallai katin INEC ne. Sanan na biyu, nau’rar zata tantance ko wannan katin da ka zo dashi na wannan rumfan zabe ne, na uku kuma shine tabbatar da cewa wannan katin naka ne, ba na wani bane. Idan wadannan basu cika ba, baza ka iya yin zabe da katin ba. Saboda haka idan wani ya sayi katin wani, to gaskiya ya bata kudin shi, ya bata lokacinshi.
Your browser doesn’t support HTML5
Duk da ikirarin raba sama da kasha 90 cikin dari na wannan katin zabe ga al-ummar Jihar Kaduna, da kwamishinan zaben yayi, har yanzu wasu jama’a na cigaba kukan cewa basu samu kati ba