Rahotanni daga Indonesia na cewa Dutsen Merapi ya sake aman wuta da aka juma ba'a ga irinta ba. Sakamakon haka,an sami karin hasarar rayukan mutane sama da 70.
Rahotanni daga Indonesia na cewa Dutsen Merapi ya sake yin wata aman wuta mafi girma da aka jima ba’a ga irinta ba.
Aman wutar da ta janyo Karin asarar rayukan mutane sama da saba’in Ma’aikatan ceto tare da agajin soja na ci gaba da kokarin zakulo gawarwakin mutane daga karkashin rubzawar gine-gine.
Jami’an Gwamnatin Indonesia sun kara tazarar nisan yankin da aman wutar ya shafa ya zuwa kilomita ashirin, an kuma samar da wuraren kula da wadanda matsalar ta shafa na gaggawa domin lura da lafiyarsu.
Ma’aikatar sufurin Indonesia ta gargadi matuka jiragen sama dasu kokarta kaucewa bi ta sararin samaniyar Dutsen da yayi aman wutar.