Jami’an nazarin bala’i sunce kusan mutane dari uku ne suka mutu a sakamakon girgizar kasar data auku a kasar Indonesia.Kuma kusan mutane talatin sun mutu a sakamakon amon wuta a tsibirin Yava. A karon farko a yau Laraba ma’aikatan agaji da jiragen sama da kuma jiragen sama masu saukar angulu suka isa tsibirran na Mentawai da suke lungu a gabar tekun Sumatra daga yammaci inda a ranar litinin girgizar kasa hade da mumunar igiyar ruwa da ta biyo bayanta suka yi awon gaba da wasu kauyuka. Shugaban kasar Susilo Bambang Yudhoyono ya katse ziyarar daya kai Vietnam ya koma gida domin nazarin aiyukan ceto. Jimmy Nadapdap shine ke lura da yunkurin aiyukan ceto na kungiyar agajin kasa da kasa World Vision. Jimmy yace a shirye suke da kayayyakin taimako. Yace suna da kayayyakin da suka adana a birnin Jakarta da kuma birnin Padang, domin su samu damar aikawa da kayayyakin abinci da ruwa da kuma kayayyakin taimakon yara cikin gaggawa.
Kuma kusan mutane talatin sun mutu a sakamakon amon wuta a tsibirin Yava. A karon farko a yau Laraba ma’aikatan agaji da jiragen sama da kuma jiragen sama masu saukar angulu suka isa tsibirran na Mentawai da suke lungu a gabar tekun Sumatra daga yammaci inda a ranar litinin girgizar kasa hade da mumunar igiyar ruwa da ta biyo bayanta suka yi awon gaba da wasu kauyuka.