Indimi Ya Sake Ginawa ‘Yan Gudun Hijara Gidaje 100

Indimi ya gidawa 'yan gudun hijira gidaje 100

Gwamnan jihar Borno ya kaddamar da rukunin gidaje 100 da Dakta Muhammadu Indimi ya ginawa ‘yan gudun hijira dake garin Bama.

Baya ga kaddamar da gidajen 100, cikin ‘yan kwanakin nan za a fara aikin gina wasu gidajen guda 100 a garin Ngala, don tallafawa ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya yabawa Dakta Muhammad Indimi game da irin taimakon da yake yiwa al’umar jihar Borno, musamman ma wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu wanda ya ce suna cikin halin kaka-ni-kayi.

Ko a shekarar 2014 sai da Dakta Indimi ya bayar da gudunmawar dalar Amurka miliyan biyar, ga wani taron liyafa na fadar shugaban kasa da aka shirya don neman hanyoyin da za a bi wajen tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

Dakta Indimi ya bayyanawa Muryar Amurka cewa kowanne gida da ya gina yana dauke da dakuna uku da dakin girki da kuma bandaki.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Indimi Ya Sake Ginawa ‘Yan Gudun Hijara Gidaje 100 - 3'05"