India Ta Ba Najeriya Dala Miliyan 100 Don Bunkasa Fannin Yanar Gizo

Web Lines

Burin Najeriya na samun kafar yanar gizo ko intanet, ya samu tallafi bayan da gwamantin India ta bayyana aniyarta ta ba kasar bashin dala Miliyan 100 domin bunkasa wannan fanni a yankunan karkara, a cewar jaridun Najeriya.

Bankin India na EXIM tare da hadin gwiwar ofishin jakadancin Najeriya da ke India da kuma ma’aikatar sadarwa ta Najeriya suka tsara wannan shiri.

Shirin kulla wannan yarjejeniyar ya faro ne tun a zamanin mulkin tsohon minista, Alhaji Adebayo Shittu wanda ya jagoranci ma’aikatar ta sadarwa, inda a can baya ya taba alkawarin cimma samar da kashi 70 cikin 100 na fasahar da za ta samar da yanar gizo a Najeriya nan da 2021.

Jaridar Guardian, ta ruwaito cewa,ana sa ran za a yi amfani da wannan bashi wajen kara himmar aikawa da na’urorin da za a dasa a filaye daban-daban a yankunan karkarar kasar.

Jami’an ma’aikatar sadarwar ta Najeriya da ke da masaniya kan wannan shiri, sun ce cikin shekara guda, za a iya dasa wadannan kayayyaki a filaye 1,000, da zaran kasashen biyu sun kammala kulla yarjejeniyar.