Bashir Ahmad wani matashi ne dan shekara goma sha biyar wanda ya ce yana matukar kaunar ya ga cewar ya gama kwarewa a sana'ar sa domin irin ra'ayin da yake da shi na son taimakawa al'uma.
A hirar su da Baraka Bashir, wakiliyar Dandalin VOA, matashin ya bayyana cewar ya fara ra'ayin koyon wannan sana'a ne daga zuwa sharar shagon telolin. Ya kuma kara da cewar irin dangantakar da ta shiga tsakanin su da masu shagon ce ta sa har suka fara koya masa aiki.
Matashin ya nuna irin ra'ayin sa akan ilimin boko sai dai a cewar sa, a yanzu bai da halin da zai iya biya wa kansa kudin makaranta amma da zarar ya gama kwarewa da koyon wannan sana'a lallai zai hada da ilimin boko domin ya taimakawa jama'a da kuma ciyar da alu'ma gaba.
Daga karshe ya yi kira ga sauran matasa maza da mata da su mike da neman na kan su domin ta haka ne kadai za su iya taimakon kan su da kuma al'uma baki daya.
Ga rahoton Baraka Bashir.