Ina Sana'a Ne Domin Cika Burin Zama Likita

Shamsiya Magaji

Wannan sana’ar ina yin tane domin tara kudaden da zan cigaba da yin karatun boko domin cika burin a na rayuwa na sama Likita in ji wata matashiya Shamsiya Magaji.

Domin a cewarta babban burin ta shi ne na zama likita domin taimakawa ‘yan uwanta mata mussamam ma a bangare lafiya ganin yadda mata ke da matukar bukatar kula dasu da ‘ya’yan su ta fuskar kiwon lafiya.

Ta bayyana haka ne ga wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, a yayin zantawarsu a birnin Kano, inda ta ce burin ta bai wuce ta samu ilimin boko ba amma a cewarta kafin nan dole sai da kudi ne ake cimma wadannan buruka shi yasa ta dukufa sana’a.

Ta ce kasancewar ‘yayenta ba masu karfi bane dole ta nemi na kanta don hucewa kanta takaici.

Shamsiyya ta ce a kullum tana toya kwanu hudu na waken soya domin yin awara, ta ce ta kamala karatunta na sakandare shekaru biyar da suka gabata , kuma a yanzu ta lulara babban cigaban diya mace sai ta nemi karatun boko.

Your browser doesn’t support HTML5

Ina Sana'a Ne Domin Cika Burin Zama Likita - 2'20"