Ina Raba Zinariyar waka - In ji Kabir Mai Zinariya

Jarumi Kabir Mai Zinariya

A fannin nishadi a yau dandali ya samu bakwancin mawaki Kabir Mai Zinariya da ya shafe shekaru goma sha biyar yana harkar waka

Mai Zinariya dai ya ce ya tsundama harkar waka ne domin ya fadakar da kuma ilimantar mussamam ma abubuwan da suka dangancin adininsa da al’ada da kuma zamantakewa matasa

Ya ce waka baiwa ce kuma hikima ce da ba kowane mutum ke da ita ba , sai mai basira da hikima ke yin waka.

Ya kara da cewa sai mutum na da ra’ayin waka ne kadai zai iya tsara baitukan waka ya kuma rera ta.

Mai Zinariya ya ce wata rana su kan samu basirar waka ne a abubuwan da ke faruwa na yau da kullum wanda kan jefa su cikin tunani da kuma bukatuwar tsara baitukan waka , har ila yau mawakin kan shirya baitukan waka a ra’ayin kansa domin ya nishadantar da kuma ilmantarwa.

Kamar yadda al’adar wannan shiri take, dandali yayi wa mawaki Mai Zinariya titsiye baiti guda ga Dandalinvoa.

A fannin tsegumi kuwa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce shirye-shirye ya yi nisa tsakanin ta da gwamnatin Nijar wajan cinikayyar fina-finai a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban hukumar tashe fina-finai Afakallahu ya ce a karkashin shinrin fina-finan da hukumar ta amince da su kadai ne za’a a iya sayarwa a jamhuriyyar Nijar.