Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunwa A Daji Sai Fantsama Cikin Gari


A yayin da kasashe daban da ban ke fuskantar kalubale da dama, wasu na fuskantar bala’in cuttutuka wasu ambaliyar ruwa, wasu kuwa masifa na yaki da ‘yan ta’adda. Sai ga wata annobar yunwa ta bayyana, ga dabbobin daji.

A wani gari mai suna Luchegorsk, na kasar Rasha, yunwa ta addabi namun daji, inda wasu dabbobi da ake kira “Bear” a turance suka fito daga cikin daji, suka shigo cikin garin, don neman abinci. Wanna garin yana kusanci da bakin iyakan kasar China, mai kimanin mutane 21,00. Mafi akasarin lokkuta wadanna dabbobin suna da wani irin abinci da suke ci, mai kama da Gyada, amma yanzu amwayi gari babu wanna abincin.

Hakan yasa sun shigo cikin gari don neman abinci, wanda har sun raunata mutane biyu, jami’an ‘yan sanda nata kai kawo cikin garin, suna korar wadanna dabbobin cikin daji, suna kuma sanar da mutane kada su fito waje balle har yara su samu damar yin wasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG