A ranar Talatan nan ne aka kai karshen rade-radin sauya shekar Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle, a wani babban taron gangamin karbar sa a APC a hukumance da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar.
Shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa, kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, shi ne dai ya karbi gwamnan a hukumance a wajen bikin, wanda ya sami halartar kusan dukan gwamnonin jam’iyyar ta APC na Arewacin Najeriya.
Buni ya daga hannun gwamna Matawalle tare da damka sa tutar jam'iyyar, wanda ya tabbatar da kalaman shugaban jam'iyyar na riko, cewa jagorancin jam'iyyar a yanzu ya koma hannun Matawallen.
To sai dai wani babban abin da ya fi jan hankalin jama’a a wajen taron, shi ne halartar tsohon gwamnan jihar ta Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar, wanda tun farko ya kalubalanci shigowar Matawalle a cikin jam’iyyar, sakamakon dadaddiyar takaddamar da ke tsakaninsu.
Gwamnan na Zamfara dai ya shigo APC ne a daidai lokacin da aka dinke babbar barakar da ta yi sanadiyyar hawansa kan mukamin, tsakanin tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari da 'yan takarar na 8 da ake yi wa lakabi da G-8, a karkashin jagorancin Sanata Kabir Garba Marafa.
To amma a wani jawabi da yayi wa wasu kusoshin jam'iyyar ta APC a Kaduna, a daidai lokacin da ake gudanar da taron na Gusau, jagoran ‘yan G-8 din Kabir Garba Marafa, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nemi alfarmar Yari ya halarci taron, amma ba don sun so haka ba.
"Gwamnan jihar Kaduna ya kira ni, yake ce min don Allah shugaban kasa na neman alfarmar Yari ya halarci taron na Gusau tare da gwamnonin APC, amma da farko munce ba mu amince da haka ba, to amma daga baya muka amince amma kuma tare da sharadi" in ji Kabir Marafa.
A cewar sa an tsara sharadin cewa da zara an kammala taron, kai tsaye daga Gusau gwamnonin za su dawo a Kaduna, inda za'a zauna tare da su, da Yari da kuma shi gwamna Matawalle, domin Tattauna yarjejeniyar baiwa kowa hakkinsa a jam'iyyar.
To sai dai kuma wani abin da ya rage wa taron na Armashi, shi ne rashin mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara, Barrister Mahdi Aliyu Gusau, wanda daga bisani kuma ya yi jawabi ta kafafen yada labarai cewar yana nan daram a PDP.
A cewar mataimakin gwamnan, tun da aka soma zancen sauya shekar gwamnan ba'a taba tuntubarsa ko sanya shi a cikin lamarin ba.
Mataimakin gwamnan wanda da ne ga tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro Janaral Aliyu Mohammed Gusau, ya kara da cewa "kowa ya san irin gwagwarmayar da mahaifi na ya yi da rawar da ya taka wajen kafa jam'iyyar PDP. Mun kasance cikinta da dadi, da ba dadi, don haka har yanzu ba inda zan je, ina nan a cikin PDP."
Haka kuma mataimakin gwamnan wanda da ma lauya ne, ya ce akwai tababa kan matakin gwamnan na ficewa daga PDP, idan aka yi la'akari da cewa ba cin zabe suka yi ba, kotu ce ta kwace mukaman ta ba su a matsayin jam'iyyar da ta fi yawan kuri'u.
A bangare daya kuma, jam’iyyar PDP ta kasa ta ce lallai sai inda karfin ta ya kare, domin kuwa za ta garzaya kotu, domin ta kalubalanci matakin gwamna Matawalle na ficewa daga jam’iyyar, da ma dukan ‘yan majalisar dokoki na jiha da na tarayya da suka bi shi.
Kakakin jam’iyyar ta PDP Ibrahim Umar Tsauri, ya bayyana ya ce "mukamin gwamnan jihar Zamfara da ma dukan 'yan majalisar dokoki na jiha da na tarayya duk na jam'iyyar PDP ne kamar yadda kotu ta ba ta."
Ya ci gaba da cewa "kotun nan da ta ba su wadannan mukaman, ita za mu je domin ta kwato mana su ta maida mana."
Saurari cikakkun tattaunawa a kasa:
Your browser doesn’t support HTML5