Ina Nan Da Raina – Shugaban INEC

Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Yakubu Mahmood

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Farfesa Yakubu ya halarci wani taron mu’amala tare da Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Zabe a ranar Laraba, 11 ga Disamba, 2024.

Shugaban Hukumar zabe ta INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce yana nan da ransa.

An yi ta ramadidin cewa shugaban hukumar ta INEC ya rasu a ‘yan kwanakin nan.

Sai dai cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Rotimi Oyekanmi ya fitar, Yakubu ya ce yana nan da ransa.

"An jawo hankalinmu kan wani labari na kmara tushe da aka yada a wasu sassan kafafen sada zumunta, inda aka yi ikirarin cewa shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya mutu a wani asibiti a London. Labarin ya fara bayyana ne a ranar Litinin, 9 ga Disamba, 2024."

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Farfesa Yakubu ya halarci wani taron mu’amala tare da Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Zabe a ranar Laraba, 11 ga Disamba, 2024.

Haka kuma, ya jagoranci taron Hukumar tare da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi a ranar Alhamis, 12 ga Disamba, 2024.