Muryar Amurka ta nemi jin ra'ayin masanin shari'a musamman fannin dokokin kasa da na aikin majalisu domin taji ko rahoton SSS nada tasiri akan wanda shugaban kasa ya wanke ya kuma nadashi kan wani mukami.
Tambaya ta biyu ita ce ko Majalisar Dattawa nada hurumin yin anfani da rahoton SSS,wadda ita ma tana karkashin shugaban kasa ne, tayi anfani da irin rahoton tayi watsi da zabin shugaban kasa.
Wani masanin shari'a yace matsayin da Majalisar Dattawa ta dauka akan Ibrahim Magu ya tayar da tambayoyi da dama har ma a ofishin shugaban kasa. Ta yaya ma'aikatar dake karkashin shugaban kasa zata kawo rahoton da zai rusa abun da shi shugaban kasa ya aiwatar.
A ganin masanin hukumar SSS ba wata bangare bace daban kamar bangaren zartaswa da ta shari'a ko majalisa. Tana karkashin zartaswa ne kuma shugaban kasa shi ne shugaban zartaswa har ma kasar baki daya. Abun mamaki ne shugaban kasa ya rubuta abu kana wani yankin dake karkashinsa ya rubuta nashi yace ba haka ba ne.
Masanin yace idan ita hukumar SSS nada wani abu daban akan shi Ibrahim Magu kamata yayi ta rubutawa shugaban kasa ya san abun da zai yi ba ta aika da nata rahoton ba zuwa waje. Kuma dole ne duk abun da zai fita waje sai shugaba ya duba ya amince kafin ya fita.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5