Ina Matasa Suke Bayan Da 'Kurar Siyasa Ta Lafa

A shirin mu na matasa da siyasa a yau ma iya cewa dara ce ta ci gida domin kuwa mun sami zantawa da abokiyar aiki 'yar jarida, malama Zulaiha Yusuf Aji, wacce rikicin zaben na zabukan gwamnoni ya rutsa da ita a unguwar Gama dake jihar Kanon Dabo.

'Yar jaridar ta kada baki da cewar, matasan 'yan siyasa da ke tururwa zuwa kafafen yada labarai na yada labaran siyasa walau domin iyayen gidansu ko don samun makafa domin cin ribar demokradiyar, yanzu sun yi shiru ba a jin duriyarsu.

Haka kuma bisa al’adar siyasa lokaci ne da matasan da ake kira "sojojin baka" na 'yan siyasa kan samu wuri su huta da zarar an kare kakar siyasa, sannan a yanzu mafi yawansu suna nan sun yi kwance suna tunanin ta ina ne zasu amfana wa kansu da kuma wadanda suke take musu baya.

Ta ce su wadanda suka kai ga gacci ba za’a sake jin babatunsu ba har sai idan sun je da bukatunsu na kashin kansu, idan kuma aka ki biya musu bukatunsu ko kuma su wadanda basu samu nasara ba sun kafa sun tsare suna sanya ido domin ganin ko gwamnatin da aka zaba shin suna ayyukan da aka bukata ko akasin haka.

Saurari cikakkiyar hirar Malama Zulaiha Yusuf Ali.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa 'Yan Siyasa Dake Zuwa Kafafen Yada Labrai Walau Don Uban Gidansu Ko Don Samun Makafa 03'57"