Ina da kwarin Guiwa A Wasan Da Wikki Zata Buga Na CAF: Baba Ganaru

Muhammed Baba Ganaru Wikki Tourist Manager

A cigaba da wasannin da akeyi na cin kofin zakarun nahiyar kasashen Afirka CAF Confederation Cup 2017, Jagoran Kungiyar kwallon kafa na Wikk Tourist, dake garin Bauchi Muhammed Baba Ganaru, yace kungiyarsa tana da kwarin guiwar samun nasara a wasan da zasuyi da Kungiyar kwallon kafa ta RSLAF, ta kasar Sierra Leone, a ranar lahadi 19/2/2017 a filin wasa na tunawa da Sir Abubakar Tabawa Balewa, dake Bauchi, a tarayyan Najeriya.

A satin da ya gabatane dai Kungiyar ta wikki, ta yi tataki zuwa kasar Sierra Leone, don fafatawa a wasan farko na CAF inda aka samu nasarar lashe wikki, da kwallaye 2-0.

A hirar da yayi da Dandalinvoa.com, Baba Ganaru, ya yi kira ga magoya bayan kungiyar ta Wikki, da su basu cikekken goyan baya a yayin wasan kuma su zamo masu bin doka da oda.

Wikki Tourist dai tana neman kwallaye ukku da babu kafin ta samu nasarar zuwa zagaye na gaba.

Your browser doesn’t support HTML5

Ina da kwarin Guiwa A Wasan Da Wikki Zata Buga Na CAF: Baba Ganaru