Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wayne Rooney Na Iya Barin Taka Leda A Manchester United


Tsohon dan wasan tsakiya na Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Scholes, ya ce yana da tabbacin kaftin din Kungiyar Manchester United, Wayne Rooney, zai bar kungirar a karshen kakar wasan Bana da zarar anbude hada hadar ‘yan wasa.

Scholes, ya ce ba abin mamaki bane idan aka ce Rooney, zai bar Manchester, duba da yadda dan wasan ya samu kansa na rashin fafatawa a wasu manyan wasanni da Kungiyar take yi a tun zuwan sabon Maihoras da kungiyar Jose Mourinho.

Wayne Rooney, ya shafe shekaru da dama a Kungiyar ta Manchester, inda ya zamo dan wasan da yafi kowa zurara kwallo a Kungiyar, Rooney ya jefa kwallaye har dari biyu da hamsin a lokacin yana ganiyarsa

Paul Scholes, yace har yanzu Rooney, yana da sauransa a kwallon kafa

kwantirakin Rooney, mai shekaru talatin da daya da haihuwa, zata kare a 2019.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG