Illar Kutse Zata Haifar Da Karancin Wayoyin Apple

Kamfanin Semiconductors, dake kerama kamfanin Apple manhajojin wayoyinsa, ya bayyana samun nasara wajen shawo kan ‘yan kutse da suka shiga wayoyin jama’a don daukar bayanan sirri. Kamfanin na sa ran za a samu tsaiko wajen samar da sinadaran hada wayoyin iPhone baki daya.

Kamfanin na kasar Taiwan, ya bayyana cewar kimanin kaso 80% na bangaren manhajar wayoyin Apple da ‘yan kusten suka raunata a jikin manhajojin wayar, wanda hakan ya basu babbar matsala a ranar Juma’a.

Ya zuwa yanzu kamfanin bai bayyana irin illar da hakan ya haifarba, har ma da wasu kamfanoni da yake kerama manhajoji, kamfanin dai ya danganta matsalar da cewar an samu hakan ne a sanadiyyar yadda ma’aikatan suka sake yayin saka manhajar a wayar.

Kamafanin ya tabbatar da cewar a sanadiyar hakan za’a samu karancin kayan hada wayar Apple, kuma za’a iya samun hauhawar kudin wayar ta Apple da ma wasu wayoyin a sanadiyar wannan matsalar.