Ilimi Ginshikin Rayuwar Dan Adam

'Yan Makaranta

Ilimi shine ginshin rayuwar in ji wata matashiyar malaman makaranta ramla Sjhehu.

Ta bayyana haka ne a yayin zantawa da wakiliyar DandalinVOA , inda take cewa rashin gine-ginen ajujuwa da dakin malamai wato Staff room na yi wa harkar koyarwa karan tsaye.

Ta kara da cewa duba da yadda matsalolin da ke tattare da harkar koyarwa rashin muhimmam kayan aiki koyarwa na dakile inganci harkar kasuwa a kasa baki daya, ko da yake ta ce ta karanci aikin jarida ne amma kasancewar yadda kasa ta ke ta tsunduma ga harkar koyarawa

Ramla ta ce tun da farko ma ba aikin jarida ta so ta karanta ba, abinda ta so karantawa shine harkar lissafi domin ta yi aiki a banki, ta ce da yake ta fara harkar karatu da wuri shigar ta jami’a ya zo da kalubale.

Ramla ta ce a harkar koyarwar kuwa baya ga tasu matsalar na rashin dakin malamai su kansu dalibai basu da ajujuwa illar na wata islamiya mai ajujuwa da ake basu aro, sai daga bisani wani bawan Allah ya taimaka ya gina musu ajujuwa biyu domin gudanar da karatun.