Dubban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Jamus suka yi tururuwa don goyon bayan dan wasan kasar, Mesut Ozil bayan da ya bayyana ajiye takalman wasansa a kasa, bisa abinda ya kira da cewar ana nuna masa "wariyar launin fata.
Magoya bayan sun taru ne a birnin Berlin, sanye da Riga wadda aka rubuta I'm Ozil, suna daga tutar kasar Jamus, da ta kasar Turkiya inda asalin Ozil Kenan suna nuna goyan bayansu ga dan wasan na kungiyar Arsenal inda yake murza ledarsa a yanzu.
A kwanakin baya ne dan wasan yace Babban dalilin sa na barin wasa a kasar shine da zarar an samu nasara a wasa to shi ya kasance dan asalin kasar Jamus a wajan wasu jama’a, amman dazarar an sha kasar a wasa sai rika ce masa dan cirani.
Sai dai hukumar kula da wasan kasar ta karyata wannan zargi inda ta ce tana kokarin kare masa mutuncinsa ako da yaushe. Ozil dai ya fito ne daga tsatson Al'ummar kasar Turkiya, ammma yana zama a kasar Jamus.
Dan wasa Ozil, ya gode wa magoya bayansa saboda "ƙauna"da suka nuna masa a lokacin wasan share fage na kakar wasanni ta bana a kungiyarsa ta Gunners, kuma ya samu goyon baya daga 'yan wasansa da kuma sabon manajan kungiyar Unai Emery.
Your browser doesn’t support HTML5