Sai An Shawo Kan COVID-19 A Iya Bude Harkoki Duka -WHO

Shugaban Hukumar lafiya ta duniya WHO ya yi gargadin cewa “babu kasar da za ta iya dauke kai kamar annobar coronavirus ta tafi.”

A lokacin da yake ganawa da manema labarai ta yanar gizo , Dr Tedros Adhanom Gebreyesus ya ce dole kasashe su mayar da hankali kan ceto yaruwar mutane idan suna so su bude tattalin arzikinsu yayin wannan annobar.

“Idan dai kasahe sun shawo kan cutar, to budewa ba zai zama matsala ba, amma a bude ba tare da wata takamammiyar nasara ba, shi ne zai janyo babban bala'i.” In ji Tedros.

Shugaban ya ayyana abubuwa hudu a matsayin abin da kasashe ya kamata su yi domin rage yaduwar cutar. A cikin abubuwan nan hudu akwai kara yawan wadanda ake yi wa gwaji, da hana mutane da dama taruwa a wuri daya da dai sauransu.