Babbar jami’yyar adawa ta PDP, a Najeriya, tace tana cikin wani hali na bacin rai game da cigaba da tsare shugabanta na jihar Barister Tanko Beji, da hukumar EFCC, ke cigaba da yi .
Yau kwanaki tara kenen dai dai da hukumar EFCC, ta kama Barister Tanko Beji, a Abuja, bisa tuhumarsa da karkatar da wasu kudade kimanin Naira miliyan Tasa’in, nay akin neman zaben gwamnan jihar da aka gudanar tun a shekarar 2011.
Babban mai bincike na PDP, a jihar Neja, Alhaji Muhammadu Gambo Suleja,yace duk binciken da suka gudanar daga Minna zuwa Abuja, ya nuna cewa Gwamnan jihar Abubakar Sani ne yace a kama shugaban PDP, na jihar domin a rufe masa baki ya dena sukar Gwamnati, Kalmar da yayi cewa APC, ta cika shekara biyu a mulki ta kasa cika alkawari ana zaune cikin wahala shi ya jawo halin da yake ciki.
A nasa martanin kakakin Gwamnatin jihar Neja, Mr. Jonathan Vastsa, ya ce wannan abun yanzu ya kasance kowa aka kama sai ace Gwamnatin Neja ce ta sa aka kama, duk wadanda suka yi mulki kafi wannan Gwamnatin jama’a sun manta da irin barnan da suka yi yana mai cewa ko lokacin da aka kama Dr. Mua'zu Babangida Aliyu, an zargi Gwamnantin jihar Neja.
Jonathan Vatsa, ya ce ba Gwamnatin jihar Neja, ta kama shi ba jami’an tsaro suka kama shi ya kara da cewa idan babu adawa siyasa bata da dadi domin shima yayi adawa.
A baya dai sau biyu ita hukumar ta EFCC, ke gurfanar da Barister Tanko Beji, a wata babbar kotu dake Minna ba tare da alkalin kotun ya saurari shara’ar ba.
Your browser doesn’t support HTML5