Ministan yada Labarai na Najeriya Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana kudurin gwamnatin tarayyar kasar na ci gaba da fafutukar ganin ta kwato dukkan kayayyakin tarihi da aka sace daga kasar zamanin mulkin mallaka zuwa kasashen waje.
A jawabinsa Minista Mohammed, ya gayawa mahalarta bikin nuna kayyakin tarihi da aka yi a Legas cewa, gwamnati tana basu tabbacin cewa ba zata yi kasa a guiwa ba wajen ganin dukkan kayyakin tarihinta da aka kai kasashen yammacin duniya da kuma Amurka an dawo da su.
Ita ma a nata jawabin wata 'yar kasar Amurka Malama Jeane, wacce take karantar da kayayyakin tarihi a jami'ar Benin, ta bayyana takaicin ganin 'yan Najeriya basa sha'war karatu kan dadaddun kayan tarihi, sun gwammace na zamanin yau.
Shugaban hukumar da take kula, da kuma adana kayayyakin tarihi Alhaji Yusuf Abdullahi Usman, yayi karin haske kan kasashe shida ciki harda Amurka da Faransa, wadanda suka maidowa Najeriya kayayyakin tarihinta.
Facebook Forum