Idan Alkalai Basu Tsare Gaskiya Ba Dimokradiya Zata Gurgunce

Wasu na ganin 'yansanda yakamata su kama alkalai ba DSS ba

Duk da bayanan da hukumar DSS ta keyi akan kamun wasu alakalan Najeriya har yanzu kawunan masana akan harkokin shari'a da gudanar da mulki ya banbanta.

Mai magana a madadin hukumar DSS Abdullahi Garba yayi bayani akan kamun da jami'ansu suka yiwa wasu alkalai bakwai da suka hada da alkalan kotun kolin Najeriya guda biyu.

Abdullahi Garba yace sun samu tsabar kudi masu dimbin yawa a gidajen alkalan banda motoci masu karen tsada iri-iri.

Gwamnatin Najeriya ta kare diran mikiya da jami'an DSS suka yiwa alkalan da nuna cewa kariya ga kowane mai mukami bai shafi maganar bincike ba musamman irin wannan yaki da cin hanci da rashawa.

Jawabin gwamnatin martani ne ga furucin babban alkalin Najeriya da shugaban kungiyar lauyoyi wadanda suke ganin matakin da aka dauka akan alkalan abun takaici ne.

Ministan gwamnati Solomon Dalung yace gwamnatin ba zata dage kafa ga yakin almundahana ba. Yace ana neman a kwace dimokradiya ne daga hannun masu mayarda dimokradiya kasuwanci.Yace zai yiwa 'yan Najeriya alkawarin cewa yayinda shugaba Buhari ya gama mulkinsa babu wanda zai sake neman wani dan siyasa ya bashi kudi kafin ya jefa masa kuri'a.

Batun cafke alkalan ya bayyana gaban majalisar dattawa da ta nuna damuwa akan diran mikiyar amma ta ture bukatar da Sanata Joshua Lidani ya kawo ta neman a gayyato shugaban hukumar DSS Lawal Daura yayi bayani.

Sanata Ubale Shittu yace matakin bai sabawa ka'ida ba amma inda so samu ne da an bar 'yansanda sun dauki matakin. Yace a fahimtarsa ba aikin DSS ba ne, aiki ne na 'yansanda. Bincike yakamata suyi kana su bar 'yansanda suyi kamu. Yace "amma dai duk wanda yayi laifi a hukumtashi"

Malamin Islama Shaikh Yakubu Musa Hassan Katsina yace yin katsalandan da gwamna Nwike yayi tare da taimakon 'yansanda wajen hana awan gaba da daya daga cikin alkalan ya nuna mahimmancin shiga lamarin da DSS suka yi.

Shaikh Hassan yace daga kan alkalin kotun koli zuwa antoni janar na kasa da babban sifeto janar na 'yansanda lallai su dauki matakin binciko wadanda suka bada kariya ga alkalin kotun Fatakwal. Yace saboda hana kama wanda yayi laifi gwamnan Rivers ya cancanta a cireshi. Shi ma kwamishanan 'yansandan jihar ya zama wajibi hukumar 'yansanda ta hukumtashi inda kuma ba haka ba to yanzu an gane alkalai da 'yansanda da jami'an gwamnati da 'yan siyasa suna son su mayarda 'yan Najeriya abincinsu.

Yanzu dai an bada belin alkalan amma kuma za'a gurfanar dasu gaban alkalai.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Idan Alkalai Basu Tsare Gaskiya Ba Dimokradiya Zata Gurgunce - 2' 54"