Hukuncin Kotu Akan Mallakar Tekun Kudancin China

Jakadan China a Amurka ya yi tir da hukuncin kotun duniya mai watsi da ikirarin China na mallakar sassan kogin Kudancin China.

Da ya ke magana a Washington jiya Talata, Cui Tiankai ya ce wannan hukucin a ta bakinsa, "zai yi illa ga aniyar kasashe ta hawa kan teburin tattaunwa da kuma tuntubar juna" don warware matsalar, kuma a maimakon hakan, zai dada janyo tashin hankali da fafatawa." To amma, in ji shi, har yanzu China ta himmantu ga tattaunawa da wadanda abin ya shafa game da takaddamar kogin Kudancin China.

Hukuncin na jiya Talata, wanda kotun mai zama a birnin Hague ta yanke ya biyo bayan karar da Philippines ta kai ne a 2013 inda ta zargi China da saba ka'aidar Majalisar dinkin duniya game da tsarin kogi, saboda takalar da ta yi ta yi a Scarborough Shoal, wanda ke tazarar kilomita 225 daga gabar Philippine.