Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata Bernie Sanders Ya Amince Hillary Clinton Ta Cigaba Da Fafatawa


Sanata Bernie Sanders mai wakiltar Vermont, wanda ya yi matukar ja da tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton,a yakin neman zama dan takarar Shugaban kasa karkashin jam'iyyar Democrat, ya hakura ya barta.

Sanatan ya amince da zamanta 'yar takarar zama shugabar Amurka karkashin jam'iyyar Democrat, wadda za ta buga da Donald Trump na jam'iyyar Republican.

Sanders ya bayyana Clinton da "wadda ta fi cancanta nesa ba kusa ba" ya kuma ce "A shirye na ke in yi duk abin da na ke iyawa in ga cewa lallai ta zama Shugabar Amurka ta gaba."

Sanders, dan shekaru 74 da haihuwa, wanda ya yi yakin neman zabensa da caccakar attajiran dandalin hada-hadar nan na Wall Street da kuma rashin daidaiton samu a Amurka, ya zayyana jerin manufofinsa na akidar sassauci da Clinton ta amince da su bayan sun shafe watanni suna kushe juna.

Sanders ya ci jahohi 22 daga 50 da aka yi zaben fitar da gwani cikinsu da kuma kuru'un rukunonin 'yan jam'iyya sabanin Clinton, to amma ta samu zama 'yar takara ta wajen nasarorin da ta yi ta yi musamman a jahohin da su ka fi girma su ka kuma fi yawan wakilan zabe ko delegates wadanda za su je babban taron ayyana dan takarar jam'iyyar daga ranar 25 ga watan Yuli.

To saidai tun ma kafin Sanders ya shiga gangamin da tawagar yakin nemar zaben Clinton ta shirya a jahar New Hampshire ta arewa maso gabashin kasar, Trump, attajirin nan mai harkar gine-gine da ke yinkurin zama zababben Shugaba a karo na farko, ya caccaki Sanders saboda amincewa da Clinton da ya yi.

XS
SM
MD
LG