Daruruwan makarantun boko ne aka rufe a yankunan dake fama da matsalar tsaro a Jamhuriyar Nijer, ganin yadda matakin ya tilasta wa dubban dalibai zaman gida ya sa mahukuntan kasar bude wasu cibiyoyin musamman a jihar Tilabery domin ‘yayan mutanen da suka kauracewa matsugunansu sanadiyar aika aikar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.
A hirar shi da Muryar Amurka, Ministan ilimi a Jamhuriyar Nijer, Dr Rabiou Ousman, ya bayyana cewa, "ya shafi fiye da dalibai 72,000 a Nijer. 'Yancin yaro ne ya samu inda za a yi karatu, shi ya sa gwamnati ta dauki wannan matakin."
Da ya ke tsokaci kan lamarin, Sakataren kungiyar malaman makaranta ta SNEN Malan Issouhou Arzika ya yaba da wannan mataki da yace abu ne da suka jima suna jiran ganinsa.
"Batun tsaro a irin wadanan wurare wani abu ne da ya kamata a maida hankali a kansa" inji Malan Issouhou.
Mahukunta na bada tabbacin daukan dukkan matakan da suka dace domin dorewar karatun yara a wadannan cibiyoyi.
Ana sa ran fadada wannan shiri domin samar da cibiyoyin karatun yaran a nan gaba kadan a jihohin Diffa da Tahoua da Maradi inda aka rufe makarantun boko da dama yayinda dubban mutane suka tsere daga matsugunansu sakamakon tashin hankalin ‘yan ta’adda da na ‘yan bindiga.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5