Hukumomin Lafiya a Gaza Sun Ce An Kashe Falasdinawa Tara

Wani Bafalasdine sanye da hular kare shakar hayaki a zanga zanagr da suke yi

Wata arangama da aka yi a karshen makon nan tsakanin dakarun Isra'ila da Falasdinawa a yankin Gaza, ta kai ga mutuwar mutane tara a cewar hukumomin lafiya na yankin Gaza.

A yau Asabar, Ma’aikatar Lafiya a yankin Zirin Gaza da ke karkashin kulawar kungiyar Hamaz, ta ce akalla mutane tara aka kashe, ciki har da dan jarida daya.

Kisan ya faru ne bayan da dakarun Isra’ila suka yi ta harbi akan masu zanga zanga, yayin wata arangama da aka yi akan iyakar yankin.

Ma’aikatar ta lafiyar ta ce, an harbi Yasser Murtaga a jiya Juma’a, wanda dan jarida ne mai daukan hoto da ke aiki da kamfanin dillancin labarai na Ain a yankin na Gaza, duk da cewa yana sanye da rigar da ta nuna cewa shi dan jarida ne.

Dakarun Israila sun ce ba za su yi wani bayani kan wannan zargi ba, domin suna kan nazarin yadda al’amarin ya faru.

Baya ga mutane tara da suka rasu a arangamar, ciki har da wani matashi mai shekaru 16, akwai kuma wasu mutane kusan 500 da suka jikkata sanadiyar harbin bindiga da dakarun na Isra’ila suka yi ta yi, a cewar ma’aikatar lafiyar ta yankin Gazan.

A jiya Juma’a dakarun na Isra’ila suka rika jefa hayaki mai sa kwalla, tare da harba harsashai na roba da kuma na gaske, domin dakile masu kokarin ketara kan iyakar Isra’ila.