Hukumomi a Kano Na Kokarin Shawo Kan Wata Sabuwar Cutar Da Ta Bulla A Jihar

Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Bayan sanar da bullar sabuwar cuta a jihar Kano a farkon wannan mako sakamakon shan lemon da ake zaton ya gurbace, hukumomi a jihar sun tashi haikan wajen daukar matakan ganin an kawar da irin wadannan lemon daga kasuwa.

Wani da ke kwance a asibiti bayan ya sha irin wannan lemo, ya fada wa Muryar Amurka yanda ya kamu da cutar da cewa, “Na je kasuwa na dawo sai na daina jin karfin jikina, da na shiga bandaki sai na ga ina fitsarin jini.”

Zaharaddin Usman ya kara da cewa, “Lemo na sha, kusan awa daya da rabi sai na ji yanayin jikina babu dadi sosai. To, da yake ranar na je bal, sai na dauka ko gajiyar bal ne da na je na dawo.”

Tun makon da ya gabata ne dai aka fara samun labarin wannan annobar zazzabi da fitsarin jini sakamakon shan wasu nau’ukan lemo. An kwantar da galibin wadanda suka kamu da cutar a asibitin cututtuka masu yado na jihar Kano.

Dakta Johnson Ocigbo, na asibitin cututtuka masu yado ya ce mafi yawan majinyatan sun ce sun sha wasu nau’ukan lemo ne. Ya ce “Sun yi korafin cewa suna fitsarin jini, dole ne mu musu gwaji, mun duba su mun ga suna da karancin jini.”

Tuni hukumar da ke kula da hakkin mai saye da sayarwar ta ji korafe korafen jama’a ta kuma kama irin wadannan lemo. Shugaban hukumar mai riko Baffa Babban Dan'agundi, ya ce sun kama buhu sama da 583 na lemon da suka lalace.

Su ma ‘yan kungiyar kasuwar Singer da Sabon Gari sun kama irin wadannan kaya a hannun ‘yan kasuwa. Shugaban kungiyar, Uba Zubairu Yakasai, ya ce shugabannin masu sayar da kayan lemon sun kwace lemon da dama suka kai ofishin KAROTA.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kano, Aminu Ibrahim-Tsanyawa ne ya tabbatar da bullar cutar a wani taron manema labarai a farkon wannan mako. Likitan ya ce mutanen da suka kamu da sabuwar cutar an kwantar da su a asibitoci 25 a fadin jihar.