Hukumomin Jihar Inugu Sun Karyata Batun Korar Fulani Makiyaya A Jihar

Korara Fulani a Inugu

Hukumomi a jihar Inugun Najeriya sun musanta rade-radin cewa an kori Fulani makiyaya daga garin Nenwe dake karamar hukumar Aninri na jihar, inda kuma hukumomin suka yi ittifakin cewa wannan mumunan sharri ne daga 'yan tada zaune tsaye.

Da yake jawabi lokacin da gwamnan jihar, Honarabul Ifeanyi Ugwuanyi da manyan jami'an tsaro suka kai ziyarar tabbatar da gaskiyar lamarin a ranar Litinin, sarkin Agbada dake garin Nenwe, Igwe Francis Imo ya nesanta al'ummarsa daga wannan zargin.

Ya ce, "Ina so in tabbatarwa dukkaninku cewa ba wanda ke korar al'ummar Fulani daga masarautar Agbada. Kuma ina so in bayyana cewa a tarihin dangantakarmu da al'ummar Fulani, ba a taba kashe wata saniya ba a wannan masarautar; kuma ba a taba raunata wani Bafulatani ba. Kuma muna ci gaba da tabbatar da zaman lafiya kamar yadda gwamna ya umurta."

Shi kuwa a nasa jawabin, gwamnan jihar Inugu, Honarabul Ifeanyi Ugwuanyi ya bayyana makasudin zuwansu garin.

Ya ce, "Muna Agbada-Nenwe dake karamar hukumar Aninrin jihar Inugu, tare da manyan jami'an tsaro da kuma wasu masu ruwa da tsaki, don tabbatar da gaskiyar lamari akan batun wani faifan bidiyon da ake ta yadawa a yanar gizo da cewar an kori wasu makiyaya da shanunsu daga wannan garin.

Toh ko me binciken 'yan sanda ke cewa a kan wannan batu?

Ga dai wakilinmu Alphonsus Okoroigwe da karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

BATUN KORAR FULANI A INUGU