Hukumomin Ghana Sun Haramta Cin Kasuwa A Bakin Titunan Birnin Accra

Wasu masu tallata hajjojinsu a bakin hanya a birnin Accra na kasar Ghana (AP)

Masu sana’ar a bakin titin birnin Accra a Ghana sun roki Ministan da ya nema musu sabon wuri kafin ya kori su daga hanyar titin.

Daga cikin matakin da Ministan birnin Accra ya dauka na tsaftace babban birnin ghana shi ne korar masu gudanar da sana’ar su bakin titi, Inda yace Jami’an tsaro zasu kama masu Sana’a bakin titi kuma su hukuntasu.

Ministan Yankin Accra, babban birnin Ghana Henry Quarty ya bukaci duk masu gudanar da sana’o’insu a bakin titi da su tashi ko kuma hukuma da kamasu kuma ta hukuntasu.

Masu sana’ar a bakin titin birnin Accra a Ghana sun roki Ministan da ya nema musu sabon wuri kafin ya kori su daga hanyar titin.

Wata kungiyar matasa da ta fara aiwatar da aiikn korar masu sana’a a babban hanyar titin Nima daga birnin Accra ta goyi bayan kudirin ministan yankin Accra.

Quartey ya ce sun hada kai da sojojin Ghana, kuma sun horas da mazaje kusan 1,000 da za su kama duk wadana suke sana’ar a bakin titi bisa tsarin doka a wani mataki tsaftace muhalli a fadin yankin Accra.