Hukumomin Faransa sun kashe mutane biyu, wadanda ake zargi da laifin kai hari

'Yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Faransa

Hukumomin Faransa sunce an kashe mutane biyu da ake zargi da laifin kai harin Charlie Hebdo kuma an kubutar da wadanda suka yi garkuwa dasu a lokacinda yan sanda suka kai sumame arewacin birnin Paris.

Hukumomin Faransa sunce an kashe mutane biyu da ake zargi da laifin kai harin Charlie Hebdo kuma an kubutar da wadanda suka yi garkuwa dasu a lokacinda yan sanda suka kai sumame arewacin birnin Paris.
Wani sumame na dabam da aka kai baban birnin kasar ya kashe wani dan bindiga da yayi garkuwa da mutane da dama a wani shago, to amma 'yan sanda sunce an kashe mutane hudu daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu a lokacinda aka kai sumamen.
Anji karajin tashin bama bamai da harbe harbe a Paris da kuma birnin Dammartin en Goele da ke arewaacin kasar a lokacinda yan sanda suka kai sumame kusan lokaci guda a jiya Jumaa.
Mujallar satirical ta birnin Paris ta bada rahoton cewa wa da kani Cherif da Said Kouachi, wadanda ake zargi da laifin kai mumunar hari a wannan mako sun fito daga inda suka buya suka fara harbi a lokacinda yan sanda suka kai sumame.
An kashe su a musayar harbe harbe tsakaninsu da yan sanda
A musayar harbe harben da aka yi a birnin Paris, jami'an tsaro sun kutsa wani shago kusa da Porte De Vincennes a wata unguwa da ake cewa unguwar Yahudawa. Sun kashe dan bindigan da ake zaton bakinsu daya da wa da kanin da aka kashe. Hukumomi sunce akwai akalla mutane biyar da aka yi garkuwa dasu, kuma an kashe hudu daga cikinsu. To amma ba'a bada dala dalan bayani ba.
A lokacinda yake zantawa da 'yan jarida, shugaban Faransa Francoise Hollande ya godewa jami'an tsaron da suka ga bayan yan ta'adan. Yayi kira ga Faransawa da su lura kuma su hada kai, daya ce sune muhimman makaman yaki da ta'adanci da nuna bambamci da kuma kyamar wani jinsi ko kabila ko addini.