Suna zarginsa da taimakawa ta'addanci, karya gameda batun shige da fice, da shirga karya wajen sayo makaman da aka yi amfani da su wajen kai harin. Yana fuskantar daurin shekaru 35 a fursina idan har aka sameshi da laifi.
Lauyar gwamnati Eileen Decker, tace, zuwa yanzu babu shaidar Marquez yana da hanu a harin da aka kai ranar 2 ga watan nan, kuma babu alamun yana da masaniya gabannin su kai harin, amma sayen makaman, da kuma kasa fadakar da hukumomi kan niyyar Farook na kai harin kan mai uwa-da-wabi, ya janyo mummunar hasarar rayuka.
Duk da cewa babu wata matsala kan sayen makaman, duk da haka masu bincike sun hakikance cewa, Marquez ya sayo makaman dalilin wata makarkashiyar da suka kulla ne da Farook a shekara ta 2012, na jefa nakiyoyi a dakin cin abinci na makaranta adakin karatu, lokacinda dalibai suka fara gudu neman tsira, su ringa harbinsu daya bayan daya.